‘Yan bindiga sun sace dan majalisa har cikin dakinsa a Najeriya
‘Yan bindiga sun sace dan majalisa mai wakiltan mazabar Nguroje da ke jihar Taraba ta Najeriya, wato Bashir Bape.
Rahotanni sun ce, an sace Bape ne a cikin daren da ya gabata a gidansa da ke birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin ya ce, ‘yan bindigan da suka yi dandazo sun fi karfin ‘yan kato da gora da ke tsaron gidan dan majalisan, inda suka kutsa har cikin dakinsa don sace shi.
Da misalin karfe daya na dare suka dirar wa gidansa akan babura a cewar rahotanni.
Wannan na dada nuni da yadda matsalar tsaro ta yi kamari a sassan Najeriya.