‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Uku Da Rana Tsaka A Katsina

Da misalin karfe ukku na ranar yau Talata, ‘Yan bindiga dauke da bindigogi sun sace dalibai ukku, ‘yan babban sakandire aji biyu na makarantar je-ka ka dawo ta Al’umma da ke garin Runka a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Majiyarmu ta ce yan bindigar sun tare su tsakanin Kililin da Gobirawa, domin yaran yan garin Gobirawa ne, suna kan kekuna ne, suka dora su kan babura suka arce da su daji.

Daliban da aka sace akwai Gaddafi Usman da Abdulrrasheed Yahuza da kuma Murtala Abdullahi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here