Advert
Home Sashen Hausa Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da...

Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, kamar yadda punch ta ruwaito.

Yayin harin yan bindigan sun hallaka mutum huɗu tare da ƙona gidajen mutane da dama, kamar yadda this day ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda ya bar mutane da dama cikin raunuka, ya faru ne lokacin mutane na bacci ranar Asabar da daddare.

Shugaban ƙungiyar cigaban Irigwe, Ezekiel Bini, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Lahadi a Jos.

Mr. Bini yace:

“Fulani makiyaya sun sake kaiwa mutanen mu hari a daren da ya gabata, amma wannan harin abin damuwa ne matuka.”

“Sun ƙona gidaje da dama a ƙauyen Zamuna da kuma gidajen dake kusa da Jebbu Miango. Sun lalata mana gonakin mu ta hanyar sassare shukoki sannan suka cinnawa gidaje wuta.”

“Zuwa yanzun an tabbatar da mutuwar mutum huɗu yayin da wasu da dama suka ji raunuka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: