Your Excellency Sir.

Saifullahi Mato
matokkr@gmail.com

Ƙura takai bango, ƴan Bindiga sun ƙwace iko da gabaki dayan yanmacin ƙaramar hukumar ƙanƙara har izuwa bakin iyakar mu da jihar Zamfara.

Kwanaki sun kone gidan maigarin Zangon ƙanƙara amma Allah ya tsare basu iske shi gidan ba.

Duk Jami’an tsaron da akace ana turawa to har yau dai bamu ga 1 ba, wataƙila kuma cikin farin kaya suke sajewa da mutanan gari.

Katse layunka waya ya taimakawa barayi wajan sake sabuwar dubarar satar mutane, in sun tare mutum 2, sai su ɗauki 1, su ba ɗaya sakon adadin kuɗin da suke so akai da inda zaa kai su.

Wani cigaba da suka samu a yankinmu har wakili garesu, in sun dauƙi mutum sai aje asameshi shikuma ya shiga daji wajansu a cinika.

Mu a yankinmu ansan dayawansu, ansan inda suke kwana. Da gari ya waye kuma suke fitowa da makamansu har zuwa cikin garin Zangon Ƙanƙara suna sayen kayayyakin da suke buƙata, har da majalisa suke hadawa kuma babu wanda ya isa ya tanka masu.

Daga Ƙanƙara zuwa Ɗansaɓau zaka samu Gate fiye da 5 na ɓarayi kullum kamar yanda ƴan sanda ke tsayawa. Abun tun yana bamu mamaki har takaimu ga miƙa wuya da fidda ran ganin ɗaukin hukuma.

Baya ga rashin noma, hatta kasuwannin mu da muke bani gishiri in baka manda suma a rufe, gashi ba’a shiga daji yo itace.

Kullum sai an sace ko kashe mana ƴan’uwan da suka rage da basu da inda zasu gudun hijira. Inma an mutun to zuwa binnewar ma aikine saboda zullumin kawo farmaki.

Koba komi ataimakemu da abunda zamu ci, yunwa ta fara kashe mana yan uwa, ga marayu kullum ana bar mana, ba makarantu saboda babu Malamin da ke iya shiga yankin ya koyar.

Munyi iya biyayya da ladabin rubutu daidak karfin mu, amma ba’a taba sauraren mu ba, don haka lokaci yayi da zamu fantsama cikin duniya da kafafen watsa labari na gida dana waje don gayawa duniya halin da muke ciki tare da nemawa danginmu gudummuwar abunda za su ci tunda gwamnati bata taɓa kaiwa yammacin ƙankara agaji ba.

Don kada wani yaga laifinmu daga baya.

HAZAH’WASSALAM

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here