Home Sashen Hausa 'Yan Bindiga Sun Kona Wani Matashi Kurmus A Garin 'Yankara.

‘Yan Bindiga Sun Kona Wani Matashi Kurmus A Garin ‘Yankara.

‘Yan Bindiga Sun Kona Wani Matashi Kurmus A Garin ‘Yankara.

@katsina city news

Rahotannin da ke shigo mana daga garin ‘yankara da ke karamar hukumar Kankarar jihar katsina, sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kona gawar wani matashi kurmus mai suna Ahmad bayan sun yi garkuwa da shi.

Lamarin dai ya faru ne a jiya Juma’a bayan ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Matashin tare da wasu Mutane.

Kamar yadda rahotonnin ke cewa, ‘yan bindigar sun kuma aike da sako ga jama’ar garin cewa, ‘Ranar Juma’a bakar rana ce ga duk wani mutumin garin Yankara’, sakon da ya daure wa mutanen garin kai.

In dai za a iya tunawa, a watan Yuni wannan shekarar 2020 ne, wani fada ya kaure tsakanin Fulani da Hausawan garin na ‘yankara, wanda ya yi sanadiyyar kashe wata mata mai suna Abu Uwar daba, matar da take da karfin fada a ji a cikin Fulanin domin ta kasance kamar matsayin uwa a garesu, wanda ake zargin wannan kisan na da alaka da wancan fadan. Da ma dai an jiyo Fulanin na cewa ba za su ta6a garin ya zauna lafiya ba.

Tun dai daga wancan lokacin da fadan ya faru ya kawowa yanzu, rigimar na ta kara zafafa, kodayake ta kan lafa a wani lokaci sakamakon sintirin jami’an tsaron da ke yi a garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: