Cikin daren jiya wasu gungun ‘yan bindiga sun afka gundumar Tursa dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto sun kashe wani mutun mai suna Mamman dan dabagi jigo a APC bisa dalilin ya tona asirin wani daga cikin su wajen jami’an tsaro.

Wasu al’ummomin garin sun tabbatarwa Jaridar Sokoto cewar, su kansu lamarin ya rutsa dasu domin ‘yan bindigar sun bi gida zuwa gida suka ba al’umma kashin tsiya.

Rahotanni sun bayyana cewar, ‘yan bindigar sun kashe tsohon kamsila Mamman dan dabagi bisa dalilin zargin cewar, ya baiwa jami’an tsaro bayani akan wani dan bindiga dake garin mai suna Bello Bori wanda jami’an tsaro suka kama daga bisani kuma suka sake shi.

Ana tinanin bayan jami’an tsaro sun sako dan bindigar ne sai yaran shi suka afka gidan Mamman dan dabagi daren jiya suka kashe shi har lahira.

Al’ummar garin Tursa sun bayyana cewar, ‘yan bindigar sun sayar da shanu goma sha bakwai da zimmar amso dan uwan su wurin hukumar, wanda aka bayyana da cewar yanzu haka ya koma daji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here