Yan Bindiga dauke da makamai sun kai hari a gidan Fada dake kan hanyar Malumfashi Yashe a cikin garinMalumfashin jihar Katsina, inda suka kashe wani limamin addinin kirista, mai mukamin rabaran da kuma sace wani rabaran din da sace mai gadi daya.

Majiyar Blueink News Hausa ta ce Rabaran din da aka kashe sunan shi Alphosus Yanshim, sun kuma sace wani rabaran din mai suna Rabaran Joseph Keke na cocin katolika. Yan Bindigar sun zo ne bisa babura, su kai ta harbe-harben mai kan uwa da wabi. Rabaran Yanshim sun kashe shi a cikin gidansa dake gidan Fada, kamar yadda ake kiran Gidan, mai gadin da ya yi niyyar taimaka masa kafin a kashe shi, sun sace shi. Shi kuwa Rabaran Joseph Keke, sun sace shi lokacin da ya fito da ya ji harbe-harben suka yi awon gaba da shi yanzu haka yana hannun su cewar majiyarmu.

Majiyarmu ta ce tuni dai aka tafi da gawar Rabaran Alphonsus Yanshim zuwa jihar Zamfara domin yi masa Zana’ida.

Da yake Tabbatar da kai harin, Kakakin rundunar’Yan Sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce tuni aka kama Mutum Biyu, kuma ana ci gaba da bin diddikin wadanda suka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here