Yan bindiga sun kai hari sansanin jami’an tsaro a jihar Sokoto

Wasu ƴan bindiga sun kai hari wani sansanin jami’an tsaro na haɗin guiwa a ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami’an tsaro a ƙalla 17.

Aminu Boza mai wakiltar sabon birni ta arewa a majalisar jihar Sokoto ne ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin kuma ya ce an kai harin ne ranar Juma’ar da ta gabata.

A cikin jami’an tsaron da suka rasu akwai sojoji tara da jami’an tsaron farar hula na civil defense guda uku da ƴan sandan Mopol biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ƙona motocin sintiri biyu sannan suka yi awon gaba da wata motar.

Har yanzu akwai jami’an tsaron da ba a san inda su ke ba.

Bbc Hausa@

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here