‘YAN BINDIGA SUN GARGADI MUTANEN DANGEZA TA BATSARI!

…su rika basu labarin jami an tsaro
Misbahu batsari
@ katsina city news

Da misalin karfe 7:30 na daren Juma’a 28/05/2021, wasu ‘yan bindiga suka shiga kauyen Dangeza da ke cikin yankin Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, inda suka rutsa da mutanen kauyen.

Sannan suka tambaye su me ya sa da jami’an tsaro suka wuce ta garin su ba su kira su sun sanar da su ba?

Da yake an ce jami’an tsaro sun kai masu hari a ranar, inda suka rutsa da su a garin Labo, kuma sun samu sa’arsu sosai.

A nan dai wasu suka shaida masu cewa ba yadda suka iya, take suka gargade su da cewa duk ranar da jami’an tsaro suka sake wucewa ba su sanar da su ba, to za su yaba wa aya zaki, kuma ma da zarar haka ta faru, to su san inda dare ya yi masu, ma’ana za su huce fushinsu a kan su, sannan suka hau baburansu suka tafi.

Bayan kura ta lafa, mutanen Dangeza na cikin Sallar Isha’i kawai sai suka ji harbi kan mai uwa da wabi, inda kowa ya yi ta kansa. Sun bindige wani matashin magidanci mai suna Nasiru Dan-gado, wanda take ya ce ga garinku nan. Dama ya yi gudun hijira zuwa Batsari, amma a ranar ya je garin abin ya rutsa da shi.

Sun yi kone-kone a garin, kuma sun yi kokarin bin mutane da harbi da nufin kisa, kazancewar lamarin ya sa tun cikin daren, mata da yara kanana suka garzayo zuwa Batsari domin su tsira da rayukansu.

Haka ma da gari ya waye hanyar garin kamar an yi kora, duk sun gudu don su tsira da rayukansu.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here