#RashinTsaro: wasu gungun yan ta’adda sun tare wasu yan kasuwa a kauyen Asarara dake gundumar Gandi karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto sun budewa mutanen dake cikin motar wuta.

Lamarin wanda ya faru da marecen ranar jiya talata inda yan kasuwar na saman hanyar su ta komawa gida bayan da suka dawo cin kasuwar Talatar Mafara dake jihar Zamfara.

Yan bindigar sun budewa duk mutanen dake cikin motar wuta sun kuma halbe mutun daya mutun biyu sun raunata yayin kuma da suka je da direban motar.

Mutanen yan kasuwar dai yan asulin karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto ne inda can ma lamarin rashin kwanciyar hankali na kara ruruwa.

Shugaban karamar hukumar Rabah Hon. Yahaya Gandi ya tabbatar da faruwan lamarin kuma ya hannunta gawar wanda aka kashe ga yan uwan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here