Daga Sadiya Umar Liman

Wasu ‘yan bindiga wadan da ba’asan ko su waye ba sun budewa Dan jarida Abdul Rahaman Abdul Rahan kuma mawallafin jaridar Hange wuta.

‘Yan bindigan sun dai budewa wata mota wadda Dan jarida yake ciki ne a hanyar sa ta zuwa garin zuru dake jahar kebbi domin yin wani aiki.

Saidai kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana sun tabbatar da cewa babu asarar rayuka ko daya amma ‘yan bindigan sun kona motar da Dan jaridar yake ciki.

Rayuwar Dan jarida Abdul Rahaman Abdul Rahaman dai tana cikin mummunan hadarin gaske inda a ko yaushe yake ta samun sakonni barazana da rayuwar sa.

©Zuma Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here