LABARI DA DUMI-DUMIN SA !

“Yan Bindiga a Jahar Sokoto Sun Rubuta Takardar Wasikar Cewar, Lallai Zasu Kai Wasu Munanan Hare-Hare a Kauyuka Hudu”

Da sanyin safiyar yau assabar 11 ga watan Satumba 2021, al’ummar kauyen Kwanar-Kimba dake karamar hukumar Dange-Shuni a jihar Sakkwato, sun ci karo da wata rubutun wasika da aka rubuta aka kuma laka a gindin bishiya domin sanar dasu harin da za’a kai musu daga yanzu zuwa kowane lokaci.

An ga rubutun takardar wasikar ne wadda ake zargin yan bindiga suka rubuta ta kuma suka laka domin al’umma su gani.

Wasikar ta ce, daga yanzu zuwa kowane lokacin yan ta’addan zasu shiga kauyukan Kwanar-Kimba, Rikina, Dange, da kuma Shuni wadanda duk ke cikin karamar hukumar Dange-Shuni a jihar Sakkwato.

Rubutun wasikar yan bindigar ya nuna cewar, “ko tarin sojoji miliyan guda ne gwamnati ta kai to ba zai hana su kai harin ba” kamar yadda zaku gani a takardar.

Wakilin mu dake a yankin ya tabbatar mana da cewar, kawo yanzu dukkan hankalin al’ummar yankunan ya tashi sakamakon barazanar yan bindigar.

“Yau mun wayi gari da wata wasika daga yan bindiga cewa, zasu shigo Kwanar-Kimba, Rikina, Dange da kuma Shuni”

“Muna kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Sakkwato da dukkan jami’an tsaron jihar Sakkwato kama daga Sojoji, yan sanda, da hukumar DSS da sauran su dasu gaugauta bincike kan rubutun wasikar sannan kuma a dauki matakan kariyar al’umma”

“Ni a cikin garin Kwanar-Kimba nake, wanda yake da nisan kilomita 4 zuwa 8 Division na sojoji dake birnin Sokoto”~Inji Awwal Bello

Awwal Bello ya ce, da hanzari suke neman a yi saurin duba lamarin tareda daukan matakan da ya dace.

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here