Yan binda biyu sun ajiye makamai a Katsina tare da mika bindigunsu
Wasu sanannun yan bindiga a jihar Katsina Sale Turwa, mai shekara 30 da kuma Muhammadu Sani Maidaji, mai shekara 33 dukkaninsu yan kauyen Illella dake cikin karamar hukumar Safana, sun gurfana a gaban gwamnan jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari da Kwamishinan yan sandan jihar Katsina da shugaban rundunar rundunar soji ta 17 dake Katsina da sauran manyan jami’an tsaro jihar Katsina, inda suka bayyana tubarsu a gabansu tare da ajiye makamansu akan abubuwan da suka aikata a baya na ta’addanci.
Kamar yadda Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya rawaito ya ce a yanzun haka sun ajiye bindigun zamani kirar AK-47 har guda goma ga Kwamishinan yan sandan jihar, inda kuma ana ci gaba da bincike