Home Sashen Hausa Yakamata musulmi su nuna basa buƙatar ƙasar Faransa acikin Al'amuransu. Inji Sheikh...

Yakamata musulmi su nuna basa buƙatar ƙasar Faransa acikin Al’amuransu. Inji Sheikh Dr Munir Sheikh ja’afar katsina

Cin Zarafin Annabi: Ya Kamata Musulmi Su Nuna Ba Su Buƙatar Ƙasar Faransa A Cikin Lamuransu. -Inji Shaikh Dr. Goni Muneer Shaikh Ja’afar Katsina.

Daga A.I Musa.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin malamin addinin musulunci na Ɗarikar Tijjaniyya da ke a birnin Katsina, Shaikh Dakta Goni Muneer Shaikh Ja’afar, a lokacin da kar6a tambayoyin tawagar manema labaru jim kadan da kammala wani jawabin Maulidi a Zawiyyar Shaikh Shareef Ibrahim Saleh Alhusaini a ranar Alhamis din nan.

Malamin yace, abin da Faransa ke yi na cin zarafin Manzon Allah wanda har shugaban ƙasar ya fito ƙuru-ƙuru ya goyi baya, to abin Allah-wadai ne kuma bai kamata al’ummar musulmi su yi shiru su ƙi ɗaukar mataki ba domin ba manzon Allah ƙasar ke ci wa mutunci ba, a’a al’ummar musulmi ne baki ɗaya suke ci wa Mutunci, wanda rashin ɗaukar wani mataki a kan hakan ke nuna cewa musulmi ba su da wata ƙima a idon duniya.

“In dai za a taɓa Manzon Allah ba a dau wani mataki ba, su ƙara yi ba a dau wani mataki ba, su ƙara yi ba a dau wani mataki ba; to abin da hakan ke nufi shi ne cewa Musulmi fa suna rage ƙimarsu ne a idon duniya.” -Inji shi

Ya ci gaba da cewa; “Al’ummar Musulmi mu hada kanmu, mu tabbata muna kishin kanmu. Wasu mutane ma da ba su kai mu ba, suna kishin addininsu ba sa so su ga an taɓa addininsu, to sai mu ace ana cin zarafin Annabi ba za mu dauki wani mataki ba?” Ya yi tambaya

Da yake ba da misali a kan irin matakin da ya kamata musulmin su fara ɗauka, ya ba da misali da cewa; yana dau a ƙauracewa duk wasu kayayyaki da ƙasar ke samarwa ko ƙerawa.

“Kasar faransar nan, ya kamata ace an yi ‘by-cutting’ din ta. Ni yanzu Motata Peugeot na rabu da ita, saboda inji wannan raɗaɗin (na cin zarafin Annabi) Na ce a rabu da ita ba na so, saboda ta ƙasar faransa ce. Na hakura da ita!” Ya jaddada

Kasar faransa dai ta yi ficce wajen cin zarafi da zanen ɓatanci ga Manzon Allah(S), inda ko a kwanakin baya sai da wata a Ƙasar ta faransa mai suna Charlie Hebdo ta yi zanen ɓatanci ga Manzon Allah, lamarin da ya kai zanga-zangogi da rubuce-rubucen kin amincewa da hakan daga sassa daban-daban na duniyar Musulmi, amma suk da haka ko ‘yan kwanakin nan an ruwaito shugaban kasar Emmanuel Macron na goyon bayan ɓatancin da aka yi wa Manzon Allah a Kasar ta faransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: