Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da Alhaji Dahiru Bara’u Mangal wajen kawo ci gaba ga al’umma da kuma rayuwar su.

Gwamnan yayi wannan kiran ne bayan da ya kammala duba aikin gina kamfanin sarrafa Takin zamani (Gobarau Fertilizer) da kuma kamfanin sarrafa Shinkafa (Darma Rice Mills) wadanda Alhaji Dahirun yake ginawa a kan hanyar Dutsinma a cikin karamar hukumar Batagarawa ta jihar Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa gina wadannan kamfanoni ba karamin alheri bane duba ga irin alfanun dake tattare dasu, kama tun daga samar da ayyukan yi ga daruruwan al’umma har ya zuwa amfani da kayan da za su samar wanda duk sun shafi rayuwar al’umma kai tsaye.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya saka ma Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da alheri, ya kuma tsare tare da inganta wadannan kamfanoni suyi tsawon zamani har illa Maasha Allah.

Gwamna Aminu Masari ya kuma kai ziyara Gidan Yara dake bayan babbar asibitin cikin garin Katsina domin duba aikin gyaran gidan da yake yi da kudin aljihun shi da nufin samun lada daga Allah Subhanahu Wa Ta’ala.

Mai ba Gwamnan shawara a bangaren ilimin yara mata, Hajia Amina Lawal Dauda ta zagaya da Gwamnan dukkan bangarorin gidan tare kuma da kara gabatar mashi da sauran koke koken gidan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here