Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga masana harkar gine gine dasu samar da wani tsari da masu karamin karfi za su iya mallakar gidaje na zamani masu aminci, ba tare da sun kashe makudan kudaden ba.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan kiran ne a yau, wurin bikin bude ofishin hukumar daidaita ayyukan injiniyoyi ta kasa (COREN) a nan Katsina.

Gwamnan ya kara da cewa yin hakan zai taimaka kwarai wajen rage yawan wadanda basu da muhalli a wannan kasa tamu mai albarka.

Ya kuma yaba masu ganin yadda cikin dan karamin lokaci suka gina Ofishi tare da bayyana cewa hakan ya nuna irin himmar da suke da ita wajen ganin sun taimaka ma wannan jiha.

Da ya juya ta bangaren tsaro kuwa, Alhaji Aminu Masari ya bayyana cewa lokaci yayi da dole al’umma za su tashi tsaye su jajirce wajen amfani da hanyoyin da suke dasu wajen kare kawunan su daga ‘yan ta’adda da suka mayarda rai ba bakin komai ba.

Ya kara da cewa ba zai yiwu mu zauna mu rungume hannuwa ba, suna shigo mu suna mana dauki daidai, mu kuma muna jiran daukin jami’an tsaro, wanda kafin su iso an mana illa.

Daukar matakin kare kan ya hada har da sa ido yaka junan mu domin gano bata garin cikin mu, masu ba ‘yan ta’adda bayanan mu, wanda hakan kuma shi ne kashin bayan duk hare haren da suke kawo wa cikin al’umma.

Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu FNIQS ya jagoranci wadanda suka rufa wa Gwamnan baya wanda suka hada da’ yan Majalisar zartaswa ta jiha da kuma wasu manyan jami’an Gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here