Advert
Home Sashen Hausa Yakamata a saka Jihar Katsina cikin jihohin da ake bawa Tallafi domin...

Yakamata a saka Jihar Katsina cikin jihohin da ake bawa Tallafi domin fuskantar ƙalubalen tsaro……Aminu Bello Masari ga Gwamnatin Tarayya

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saka jihar Katsina cikin jihohin da take ba tallafi domin tunkarar kalubalen rashin tsaro.

Gwamnan yayi wannan kiran ne a yau, a Gidan Janar Muhammadu Buhari fadar Gwamnatin Jihar Katsina yayin da ya amshi bakuncin Ministan yada labaru Alhaji Lai Mohammed da ya kawo ziyarar aiki Katsina.

Gwamna Masari ya kara da cewa jihar tana kashe makudan kudade wajen tallafa ma hukumomin tsaro da suke aiki a sassa daban daban na jihar, wanda ba don wannan tallafin da Gwamnatin ke bayarwa ba, tabbas da ayyukan sun tsaya cik.

Da haka ne, yayi kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayyar da ta waiwayo jihar Katsina ta kuma rika bada kudin da za su rage wa gwamnatin nauyin da take dauka ta bangaren tsaron.

Gwamna Aminu Bello Masari ya kuma bayyana cewa, a taron baya-bayan nan da sukayi, Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da kuma Gwamnan Jihar Naija, sun amince da su horar da ‘yan kungiyar sintiri na sa kai mutum dubu ukku kowace jiha domin karfafa wa jami’an tsaro kan yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

Shi kuwa a nashi jawabin, Minista Lai Mohammed ya bayyana wa Gwamna Masari cewa ya taho ne da tawagar manema labaru daga kafofin yada labaru sama da ashirin (20) domin suji ta bakin Gwamnatin jiha kan kokarin da take yi wajen yaki da ta’addanci domin yawanci irin labarun da suke fita daga jihar ba masu dadi bane. Kuma kai tsaye mutum zai iya gane rashin kwarewa ko son rai a yadda ake yada labarun, domin mafi yawanci bangare daya ake dauka, ba a daukar bangare ko matakan da Gwamnati take dauka.

Wannan ya sanya suka yanke shawarar tahowa domin suji da kunnuwan su kuma su gaya ma duniya.

Maimartaba Sarkin Katsina Alhaji AbdulMumini Kabir Usman, wanda yayi jawabi a madadin masarautun Katsina da Daura, ya bayyana cewa akwai alamun cewa masu ta’addanci za su iya shigowa cikin garuruwa domin sayen gidaje ko filaye, wannan ya sanya aka gargadi Hakimai, Magaddai da Masu-Ungunni da su tabbatar ana tantance duk wani da yazo da bukatar sayen gida ko fili domin kaucewa zaunar da bata gari cikin al’umma.

Taron ya sami halartar Babban Jojin Jiha Maishari’a Musa Danladi Abubakar, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da wakilan Majalisar zartaswa ta jiha da Shuwagabannin hukumomin tsaro dake nan Katsina.

Haka kuma akwai Masu Martaba Sarakunan Katsina da Daura, Alhaji AbdulMumini Kabir Usman da Alhaji Umar Faruk Umar, Hakiman kananan hukumomin da hare haren yafi kamari, sai kuma Daraktocin Mulki na kananan hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: