An yi kira ga hukumar kula da shige da fice ta kasar nan da ta kara kaimi da sa ido sosai a kan iyakokin kasar nan, musamman ta hanyoyin da ba sa cikin jaddawalin hanyoyin da hukuma ta amince dasu.

Gwamnan jiha Alhaji Aminu Bello Masari yayi wannan kira da yammacin yayin da yake karbar bakuncin Shugaban Hukumar Shige da fice ta kasa (Nigeria Immigration Service) Alhaji Muhammad Babandede a Ofishin shi dake Gidan Janar Muhammadu Buhari fadar Gwamnatin Jihar Katsina.

Gwamnan ya kara da cewa, kusan dukkan illahirin makaman da ake ta’addanci dasu, ana shigo dasu ta iyakokin mu da kasashen waje ta barauniyar hanya. Duba da yanayin fadin kasa da tsawon iyakokin, ya zama wajibi ga hukumomin da abin ya shafa su hada karfi da karfe domin shawo kan fasa kwaurin makamai da zirga zirgar marasa gaskiya da ‘yan ta’adda.

Alhaji Aminu Masari ya kuma yabawa wa hukumar saboda yadda ta maida dukkan ayyukan ta a kan yanar gizo, wanda hakan ya rage laifukan da ake yi musamman wajen bada fasfo da kuma ayyuka makamantan shi.

Tun farko a nashi jawabin, Alhaji Muhammad Babandede ya shaida wa Gwamna Masari cewa ya zo jihar Katsina domin ziyartar ma’aikatan hukumar domin gane ma idon shi halin da suke ciki da kuma yanayin yadda suke gudanar da ayyukan su. Ya kuma yi godiya ta musamman, a kan irin taimako da gudummawa da Gwamnatin Jiha ke ba hukumar akai akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here