Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Kasuwar kayan gwari

Ƙungiyar ta AUFCDN wadda ɓangare ne na ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa wato NLC, ta fara yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan ƙarewar wa’adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata buƙatunta.

Ƙungiyar na neman a biya ta diyyar naira biliyan 475 sakamakon ɓarnar da aka yi wa mambobinta a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma kashe Hausawa ‘yan kasuwa da aka yi a rikicin ƙabilancin da ya auku a kasuwar Shasa ta Jihar Oyo.

Haka nan ta buƙaci a janye dukkan shingen duba ababen hawa daga kan manyan tituna, inda ake cin zarafin mambobinta ta hanyar kaɓar kuɗi daga hannunsu.

Yajin aikin ya sa an tsayar da duk wata jigilar kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu, waɗanda suka haɗa da dabbobin yanka da kuma kayan miya.

Rahoton jaridar ya ce mahautan da ke da naman a jihohin kudu sun yi amfani da wannan damar sun tsauwala farashi, su ma masu kayan miya ba a bar su a baya ba, inda farashinsu ya tashi sosai.

Akasarin kayan abinci da suka haɗa da nama da kayan gwari, ‘yan kasuwa ne kan yi safararsu daga arewacin ƙasar zuwa kudanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here