Shahararren Mawakin Siyasar nan Dan Asalin Jihar Katsina mazaunin Kano da akafi sani da Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya Fito da wasu manyan motoci Safa, na Club din Ƙwallon sa, kuma ya umarta da duk inda mutane suke so akaisu kyauta. Rarara yayi haka ne domin ragewa Al’umar jihar kano radadin yawo kasa sakamakon yajin aiki da Ƙungiyar Adaidaita sahu, masu haya da Mashin mai kafa 3 suka shiga. Yajin aikin da suka fara a jiya Litanin ya biyo bayan sabunta Lamba da hukumar KAROTA ta umarda da suyi..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here