YAJIN AIKIN YAN ADAIDAITA SAHU A BIRNIN KANO

Kai tsaye daga unguwar Hotoro Ɗan Marke, yadda jama’a suka yi carko-carko sakamakon rashin abin hawa.

Wasu daga ciki Ɗalibai ba su sa mu damar zuwa Makaranta ba.

Na zanta da wani Dalibi mai suna Abdurra’uf Usman, dalibin aji hudu a makarantar sakandire ta Sabuwar kofa, wanda shi ma bai samu abin hawa ba.

Abdurra’uf ya ce, hukumar Karota ita ce musabbabin wannan yajin aikin, don haka yana kira ga gwamnati ta shiga lamarin don ba su damar ci gaba da karatu.

Abubakar Sidi, dalibi Jami’ar Bayero aji kusa da karshe ya shaida wa Dabo FM cewa rashin abin hawa ne yasa har yanzu bai tafi ba, kuma ya tabbatar da cewa bai zai iya yin tafiyar Naira 200 a ƙafa ba saboda nisan tafiyar

Abubakar ya tabbatar da cewa suna kan rubuta jarrabawa ne a wannan lokaci, don haka ya yi kira ga gwamnati da ta dubi lamarin na su.

Bala Goro, wani matukin Adaidaita Sahu a unguwar Hotoro, ya tabbatar wa Dabo FM cewa suna alfahari da wannan yajin aikin, domin nuna wa Gwamnati adawa da irin yadda Hukumar KAROTA ta ke cajarsu.

Sannan ya ce suna kira da Gwamnati da a soke kudin lamba, da kuma dubu 18 da Hukumar Karota ta ke karɓa, sun yarda kullum za suna biyan Naira 100, maimakon biya a dunkule.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here