‘Yan bindiga sun dasa nakiya a digar Jirgin kasa a Rijana inda daga bisani kuma suka budewa jirgin wuta. Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Rigasa a jihar Kaduna.

Daya daga cikin fasinjoji dake cikin jirgin Yahuza Getso ya shaida mana cewar maharan sun yi yunkurin kashe matukin jirgin amma da yake gilashin gaban jirgin mai karfi ne basu samau damar huda gulashin nan take ba.

A haka duk da harbin da ‘yan bindigar suka finga yiwa jirgin, matukin jirgin yayi kokarin ganin ya kai jirgin zuwa Rigasa a johar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here