Advert
Home Tarihin Unguwannin Katsina da Kewaye YADDA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA CIRE SARKI ABUBAKAR DA SARKI YERO SARAUTA...

YADDA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA CIRE SARKI ABUBAKAR DA SARKI YERO SARAUTA A KATSINA

YADDA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA CIRE SARKI ABUBAKAR DA SARKI YERO SARAUTA A KATSINA.

Sarkin Katsina Malam Abubakar a wata tafiya Rangadi

Musa Gambo Kofar Soro @Katsina City News

Bayan Turawan Mulkin Mallaka sunci Sokoto da Yaki. A Ranar 28 ga watan Maris 1903, Sarkin Katsina Abubakar ya samu sako daga Lord Lugard cewa ya shirya ya tarbi Turawa ga su nan zuwa Katsina. A Ranar 28 ga watan Maris shekarar 1903 Lord Lugard ( High Commissioner Northern Nigerian Protectorate) ya zo Katsina, bayan ya karasa nadin Sultan Attahiru na biyu a Sokoto, Sultan Attahiru shine Sarki na farko Wanda Turawan mulkin Mallaka suka fara nadawa.

A Kofar YANDAKA ne Sarki Abubakar (1887-1905) ya Mika wiya (Mubayaa) ga Turawa ba tare da anyi fada ko yaki ba. Washe Gari Lugard ya aika aka Kira Sarki Abubakar ya sake nadashi, ance Lugard ya dauki Takobin da Korau ya yanka Sanau, wannan ya nuna cewa mulki da Ummarni ya tashi daga Sarkin Musulmi a Sokoto ya Koma ga Turawan Mulkin Mallaka.

A cikin shekara 1905 ne Turawan mulkin Mallaka suka tube Sarki Abubakar daga Sarauta. Wannan kuwa ya faru ne akan wasu dalilai da suka faru tsakaninsa da Turawan Mulkin Mallaka. Kamar yadda Dr. Waisu Iliyasu ya bayyana acikin Littafin shi Mai suna (A political and Social History of the Dallazawa Dynasty) yace Turawa sun nemi Sarki Abubakar daya canza Dokokin Musulunci zuwa tsarin Turawa, wannan dalilin ya kawo sabani tsakanin Turawa da Sarki Abubakar dama wasu sauran Yan Majalissar Sarki. A shekarar 1905 ne Turawa suka tube Sarki Abubakar daga Sarauta. Turawa sun zargi Abubakar akan cewa an hada Kai dashi an kashe Kare an jefa a Rijiyar da Mr. Oliver Katsina resident yake Shan ruwa. Bayani cire Abubakar sai Turawa suka tafi da shi Ilorin daga baya aka dawo da shi Kano, a Kano ya rasu. (Waisu I. Political History of Dallazawa page 195).

SARKI YERO

Bayan an tube Abubakar daga Sarauta a shekarar 1905 sai Turawa suka nada dan’uwan shi watau Malam Yero.

Sarki Malam Yero yaci gaba da mulki tare da Yan mulkin Mallaka har zuwa shekarar 1906. A shekarar 1906 ne Turawan Mulkin Mallaka suka cire Sarki Yero. Babban dalilin cire Yero shine, ance a Ranar 16 ga watan February 1906, Turawan mulkin Mallaka na Katsina suka samu sako daga Kano province cewa an samu tawaye a Sokoto watau Satiru revelluon, sabo da haka ya Zama wajibi a kansu sukai dauki ki gudunmuwa Don murkushe Yan tawayen Sokoto. Turawa suka tashi daga Katsina suka tafi Sokoto. A lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka dawo Katsina sai suka tarar da an lalata Barikin su, an wawashe kayan su da barna iri-iri Saboda haka Turawa sun nemi Yero da yayi bayani sannan yasa a gyara Barikin cikin lokaci. Wannan shine babban dalilin daya hada Yero da Turawa. Akan hakane suka tube Yero daga Sarauta Kuma suka tafi dashi Lokoja a shekarar 1906. Bayan tube Yero ne sai aka ba Muhammadu Dikko riko Sarkin Katsina a shekarar 1906. An nada Sarki Dikko a Ranar 25 ga watan Janwari 1907. (Hull RW. The development of Administration of Katsina Emirate Northern Nigeria 1887-1944) page 47.

Reference. The development of Administration of Katsina Emirate Northern Nigeria 1887-1944. Richard Willing Hulls.

2. A political And Social History of the Dallazawa Dynasty. Dr. Waisu Iliyasu Safana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: