Yadda Rusau Yamaida Magidanci Kwana A Filin Allah A Kaduna

Yadda Rusau Yamaida Magidanci Kwana A Filin Allah A Kaduna

Mista J S Nzeeka wanda aka fi sani da Sannu-Sannu ya sha wahala ne sakamakon rusa masa gida da gwamnatin jihar Kaduna tayi

An rusa masa gidansa ne a ranar 25 ga Fabrairu 2021 wanda da Hukumar Bunkasa Tsarin Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) tayi.

A wata hira da jaridar DAILY EPISODE, Sannu-Sannu ya bayyana yadda ya mallaki fili ta hanyar ma’aikatar sadarwa ta tarayya ta hanyar Nitel tun a ranar 26 ga Maris 1986

Mista Sannu-Sannu an ba shi filin ne saboda tona asirin wata badakala da yayi a maikaitar ta Nitel. Shugaban farko na reshen yankin na Nitel Kaduna, Eng Etikudor ta hannun babban manajan sa Isaiah Muhammed kamar yadda yake kunshe a cikin wata wasika da aka baiwa jaridar majiyar mu.

Mr sannu-Sannu yayi gina bisa tsarin kamar yadda aka umarceshi yayi a cikin takardar, ya fara kasuwancin sa a cikin ginin inda daga baya ya mayar dashi zuwa na zama da na kasuwanci.

Kuma an rushe ginin ba tare da sanarwa ba kamar yadda Sannu Sannu ya shedawa jaridar Daily Episode.

 

Tsarin shine inda yake zaune, kuma yana aiwatar da kasuwancin sa don samun abin biyan bukata.

gwamnatin jihar kaduna galibi suna rusa gine-gine ba tare da samun cikakkun bayanai game da yadda mutum ya mallaki filin ba, tsawon lokacin da ya dauka yana gina da kuma yadda waɗanda abin ya shafa za su rayu cikin kunci da wahalar rashin muhali.

Mista Sanu-Sannu ya cigabada rayiwa ne a filin gininsa tun ranar da mutanen KASUPDA suka rusa gininsa.

Dukda daya daga cikin ma taimakon gwamnatin jihar kaduna ya riske ni, saidai bai fadamin sunansa ba, mutumin kuma yayi alkawarin dawowa bayan ya nuna masa hujja da kuma dalilina na zama a nan, amma bai dawowa kamar yadda yayi alkawari.

Ina neman adalci daga gwamnati Jihar, ko sake gina min gidana ko a biya ni saboda rayuwa na yi min wahala.

Akwai sauran bayani

©Daily Episodes Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here