Yadda Na Kwashe Shekaru 17 A Masana’antar Fina-finai Ta Kannywood, Cewar Jaruma Hadiza Muhammad

Hajiya Hadiza Muhammad da aka fi sani da Saima

..ni da Saima Muhammad kawaye ne kawai ba yan uwa ba

Tambaya: Za Mu So Mu San Takaitaccen Tarihin Jaruma Hadiza Muhammad.

Salamu alaikum, sunana Hadiza Muhammad kuma a kan yi min inkiya da Hadizan Saima. Ni ‘yar Kano ce, an haife ni a Fagge amma na girma a unguwar Brigade, na yi karatun firamare da sakandire wanda daga nan ne kuma na yi aure har Allah ya albarkace ni da samun ‘ya‘ya biyu. Daga baya ne kuma bayan mun rabu da mijina sai Allah ya sa na tsinci kaina a masana’antar fim.

Tambaya: Shin kina da alaka ta jini da jaruma Saima Muhammad, in aka lura da lakabin da ake mi ki da Hadizan Saima?

Amsa: Lallai ina da alaka ta jini da Saima mana tunda Musulma ce kuma nima musulma ce, amma dai dangantakar mu shi ne mu kawaye ne, kuma Allah ya zo ya hada mu a masana’anta daya, amma ba ‘yan uwa bane na jini kamar yadda mutane suke cewa ya da kanwa ne.

Kuma ita ta riga ni shigowa wannan masana’anta, hasali ma ita ce ta zamar min tsani na shigowa wannan masana’antar, domin ita ta ringa hada ni da abokan aiki har aka san ni aka fara aiki tare da ni.

Tambaya: A Matsayinki na mace, wane irin kalubale ki ka samu musamman daga wajen iyaye da ‘yan uwa a lokacin da ki ka shiga harkar fim?

Amsa: Gaskiya ni ban fuskanci wani kalubale ba, saboda kusan na shigo wannan masana’anta ne da girma na, ba wai yarinya ‘yar karama ba kamar yadda wasu suke shigowa a yanzu, tunda har na yi aure na haihu kafin na shigo. Kawai da na ga harkar fim akwai abubuwa da dama da suka ja hankalina wanda nake ganin nima zan iya ba da gudummuwa ta. Sannan abu na biyu kuma sana’a ce da iyayena kullum suke sa ka min albarka, suna yi min addu’a idan zan fita, kuma suna min sannu da zuwa idan na dawo daga aiki.

Tambaya: A Lokacin a ki ka shigo wannan masana’anta ta Fina-finai wanene fim din ki na farko da ki ka fara yi?

Amsa: Fim di na na farko, akwai wani fim da muka yi mai suna “Sakar Zuciya” amma fim din na ‘yan kungiya ne a lokacin ana kungiyoyi na dirama, to a wannan lokacin su ‘yan kungiyar su suka hada wannan fim din, shi ne dai kusan fim dina na farko wadda aka fara saka min na’urar hoto (camera).

Tambaya: Wannan Fim na “Sakar Zuciya” kina ganin kamar shi ne salar haskawarki duniya ko akwai wani fim wanda shi ne ya zama salar Haskawar Jaruma Hadiza Muhammad?

Amsa: To kusan wannan fim na Sakar Zuciya ma shi bai fita kasuwa ba, iyakacinsa gidajen sinima domin a lokacin ana amfani da sinima ne, amma dai ina fadar sa ne saboda shi ne kusan farko. Amma bayan shi gaskiya akwai finafinai da yawa wanda suka fita kusan lokaci daya, wanda zan iya cewa su ne suka zama silar da aka sanni sosai. Amma bazan iya kama sunan wani fim guda daya ba in ce shi ne ya zama silar haskawa ta, saboda finafinan suna da yawa kamar yadda na fada a baya.

Tambaya: Zuwa yanzu kin samu kamar shekaru nawa cikin wannan masana’anta ta Fina-finai Kannywood?

Amsa: Yanzu na samu kusan shekara goma sha shidda zuwa goma sha bakwai a cikin wannan masana’anta ta Kannywood

Tambaya: Duba da Irin wannan shekaru da ki ka dauka a cikin wannan masana’anta, zuwa yanzu kin fara yin Fim mallakin ki ne ko dai har yanzu kina fitowa ne a matsayin jaruma?

Amsa: Gaskiya na yi a baya amma na hadin gwiwa ne, amma insha Allah nan da dan lokaci kadan zan fara yin nawa na kaina, mallakina ba tare da hadin gwiwar wasu ba.

Tambaya: Ya ya za ki bayyana alakarki da daraktoci da Furodusoshi da kuma Sauran jarumai abokan aiki?

Amsa: Alhamdulillah, Muna mu’amala ta arziki, muna mutunta juna, komai kankantar mutum in ya zo a kan aikin sa ina mutunta shi nima ana mutunta ni. Saboda haka a iya sani na har zuwa yanzu ba ko mutum daya da zai ce ina da wani sabani da shi, daga daraktocin da furodusoshin da kuma jaruman. Muna rayuwa ta mutunta juna, kuma muna aiki cikin farin ciki muna yi wa juna san barka.

Tambaya: Wacce shawara za ki baiwa mata masu sha’awar shiga sana’ar Fim?

Amsa: To har kullum dai, kamar mu da muka dauki fim a matsayin sana’a gaskiya muna martaba fim, kuma muna kokarin mu ga mun kare mutuncinmu da na addininmu da na al’adarmu. Sabanin wasu yara kanana da suke kallon kyale-kyale na fim suke so su shigo don cin ma wata manufa. Bance duka ba, amma wasu daga ciki, wanda suna daya daga cikin wanda suke zuwa su dagula mana masana’antar nan, suke jawo mana zagi, sai mace daya ta je ta aikata wani laifi, amma sai a yi mana kudin goro a zage mu gaba daya, a yi mana mummunar fahimta. A sakamakon haka yanzu hukumomi sun tashi tsaye domin tace duk wata wadda take shirin shigowa wannan sana’a. An shigo da tsari na sai an samu amincewa daga gidanku, mai unguwarku ya saka miki hannu, sannan za a baki shaidar shigowa wannan masana’anta, sannan a fara saka ki a cikin fim.

Tambaya: Wace shawararki ga ‘yan uwanki jarumai wajen kula da mutuncin su da kuma mutunta sana’arsu. Duba da Irin rikicin da ya barke a kwanakin baya tsakanin jaruma Hadiza Gabon Da Jaruma Amina Amal?

Amsa: To ku san ba masana’antarmu kadai ake samun rikice-rikice ba, kamar yadda na fada kusan duk duniya indai mutane za su hadu to za a iya samun rikici ko zaman lafiya. To wannan wani abu ne da ya shafe su kusan mu bai shafe mu ba. Wani rikici ne da za su iya zama su sulhunta kansu. Kuma zuwa yanzu an tsawatar musu iya tsawatarwa, yadda wani ma zai ji shakka ko tsoron aikata wani abu irin wannan.

Tambaya: Wane sako gare ki ga masoyan ki?

Amsa: To masoyan mu dai har kullum muna gode mu su kuma muna musu fatan alkhairi kamar yadda suke mana. Wadanda muka sani da wadanda muke waya da wanda ma ba za mu ga juna ba har abada, muna musu fatan alkhairi mun gode da kaunar da suke nuna mana, kuma Allah ya bar zumunci a tsakaninmu. Muna roko da su ci gaba da yi mana addu’a, kuma duk inda suka ga mun yi kuskure to su sanar da mu, domin babu wani dan Adam da baya kuskure, kuma a shirye muke da mu karbi gyara, mun gode sosai.

Mun Gode kwarai Da Gaske

Nima na gode

Madogara: Leadership A Yau

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here