Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 24 bayan sun ci abinci mai guba.

Kwamishinan Lafiya na jihar Dr Ali Inname, wanda ya tabbatar da labarin a cikin wata sanarwa, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Danzanke da ke ƙaramar hukumar Isa.

Ya ce mutanen sun ci abincin ne da aka yi kuskuren amfani da gishirin lalle a madadin gishirin abinci.

“Kuma dukkanin iyalin gidan, abincin ya yi ajalinsu, mata biyu ne kawai ke raye waɗanda suka ɗanɗana abincin,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce yanzu haka ana kula da lafiyarsu a asibiti tare da cike da fatan za su rayu.

Ya ce an yi ƙoƙarin ceton ran waɗanda suka ci abincin mai gishirin ƙunshi amma Allah bai nufa ba.

Ya ce yana da matukar mahimmanci ga jama’a su san cewa lamarin da ya faru ana iya magance shi domin ba al’amari ba ne da ke yaɗuwa, saboda yana da matuƙar hatsarin yin kisa, koda kuwa an ba da kyakkyawar kulawar asibiti ga waɗanda abin ya shafa, Katsina Daily Post News ta rawaito labarin daga BBC Hausa.

Dr Inname ya ce ya kamata wannan ya zama darasi ga al’umma wanda sau biyu kenan hakan na faruwa a bana bayan al’amarin da ya faru a jihar Zamfara.

Abin da ya kamata a kiyaye

A cikin sanarwar da Kwamishinan Lafiya na jihar Sokoto ya ja hankalin jama’a tare da bayar da shawarwari ga hanyoyin kaucewa sake aukuwar wannan mummunan al’amari.

Daga cikin shawarwarin sun haɗa da keɓe kayan abinci daban da kayayyakin da suka shafi aikin gona da shafe-shafe musamman sinadarai.

Ya kuma ce yana da kyau a duba da tabbatar da kayan abinci kafin amfani da su a girki.

Dole ne a keɓe tare da kiyaye abincin da aka dafa da kuma ruwan sha.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here