Kallo ne ya koma sama a wajen rantsar da Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuka Soludo a yau Alhamis, bayan da matar gwamna mai barin-gado, Obelechukwu Willie Obiano, ta tsinka wa Bianca Ojukwu mari a bainar jama’a.

Wakilin Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan da Soludo ya ɗauki rantsuwar kama aiki.

NAN ya ruwaito cewa manyan baƙi suna zazzaune lokacin da mai-ɗakin Obiano ta shigo.

Ta na shigo wa, ta na taku ɗai-ɗai sai ta nufi sahun gaba inda mai-ɗakin Ojukwu ke zaune, inda sa zuwan ta sai ji aka yi tas!, wato ta kashe ta da tafi.

Lamarin ya ja hankalin jami’an tsaro da kuma sauran manyan baƙi, waɗanda su ka yi maza su ka janye matar Obiano da ga kan Bianca, wacce a ka hango ta cika da mamaki.

Da ga nan ne sai a ka fice da matar Obiano da ga wajen taron, inda da ga bisani mijin nata ya bi bayan ta, bayan an rantsar da sabon gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here