Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya wanda shi ne ke jagorantar ayyukan leken asiri ya yi matukar taka rawa wajen tarwatsa sansanonin Boko Haram da kuma ISWAP.

Cikin wani rahoto da jaridar PR Nigeria ta wallafa wadda ke da kusanci da sojojin kasar ta ce, shi ne ke jagorantar tawagar Lafiya Dole lokacin da Attahiru ke matsayin babban kwamanda a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ta ruwaito cewa lokacin da wasu mayakan Boko Haram su ka yi kokarin mika wuya domin tuba, shi ne ya gayawa Attahiru cewa a barsu cikin sansanin Boko Haram domin su zama masu yi masu leken asiri.

Kuma hakan ya bayar da dama wajen gwara kan kungiyoyin biyu na ISWAP da Boko Haram wanda ya kai ga babbar rashin jituwa tsakaninsu.

Kuliya na cikin wadanda suka jagoranci sauya wa rundunar Operation Lafiya suna zuwa ‘Operation Hadin Kai’ da nufin samar da hadin kai tsakanin tubabbun mayakan Boko Haram da sojoji.

An yi hakan ne da nufin samun bayanan sirri da za su bayar da damar murkushe kungiyoyin biyu na Boko Haram da ISWAP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here