Yadda Dan Uwa Ya Yi Garkuwa Da ‘Yar Shekara Ukku Har Ta Rasu A Katsina

Wani abun mamaki ya faru a karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, inda wani dan uwan wata karamar yarinya yar shekara ukku da haihuwa, Amina Tukur Dan Ali ta gamu da ajalinta a hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda mahaifin yarinya, Tukur Dan Ali ya shaida wa gidan Talabijin na Arise ya ce su wadanda suka yi garkuwa da ita, wanda ake zargin ya kasance dan uwa ne, ya nemi a ba su kudin fansa har naira Miliyan Biyu, idan ba mu kawo ba za su kashe ta. Wani abu ya sanya da ni da wani dan uwana muka shiga wani gidan dan uwanmu, sai muka fari jin wari, muna shiga gudan dakin sai muka ji warin ya Karu, sai muka ga jini a kasan wata kujera, muna leka cikin kujerar muka iske ta an daure mata baki da tsumma da wuyanta, kuma har ta rasu.

Tuni dai yan sanda a jIhar Katsina suna ci gaba da binciken lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here