Yadda budurwa ‘ta sha ƙwaya’ ta mutu a gidan saukar baƙi na gwamnatin Yobe-bbc hausa

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ƙwaya ce ta yi sanadin mutuwar matashiyar nan ƴar shekara 18 da aka tsinci gawarta a masaukin baƙin gwamnatin Yobe, da ke Damaturu.

Wata sanarwa da ta fitar ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Yoben, ASP Dungus Adul-Kareem, ta ce bincikensu ya tabbatar da cewa matashiyar mai suna Bilkisu Ali ta mutu ne sakamakon ƙwankwaɗan ƙwaya.

A ranar 7 ga watan Janairun 2021 aka cafke mutane 4 da ake zargi da alaka da aikata kisa kan matashiyar.

Sai dai an tsare su tare da mika gawarta asibiti domin binciken gano sanadin mutuwarta.

Yanzu haka dai za a mika mutanen 4 da ake zargi gaban kotu domin amsa tuhume-tuhume da ake musu wanda ya kunshi haɗa-kai wajen aikata mugun laifi da kisan-kai da zina.

Rundunar ƴan sanda Yobe ta kuma gargaɗi masu yaɗa jita-jita da su guji yaɗa maganganun da za su kasance matsala ga dangin yarinyar da aikin jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here