Wadannan Mutanen Ƴar matankari ne dake cikin ƙaramar Hukumar mulkin Anka ta jihar Zamfara bayan da Barayin Daji suka kaimasu hari.

Alummar yankin sunata roƙon Gwamnati data kai masu Ɗauki da Jami’an tsaro kusan sama da ƙwana Talatin 30 kenan bayan da wasu Yaran Fulani sukayi masu Barazanar hanasu zama Lafiya a yankin.

Shidai wannan ƙauyen bai wuce tafiyar kilometer Ashirin ba 20 daga Anka.

Kodai cikin ƙarshen makon nan an kai Hari a Zurmi Inda aka kashe Gwamman Mutane, wanda har ya jaza Gwamnatin Jihar bada dama ga Al’ummomi su kare kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here