Yan crypto sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 20 a rana guda yayin da farashinsa ya fadi kasa da dala dubu 40 a karon farko tun ranar 16 ga Maris, lamarin da ya kai ga kassara kusan ‘yan kasuwa 150,000 a kasuwar.

Faduwar farashin bitcoin na zuwa ne a daidai lokacin da masu zuba jari ke auna hadarin hauhawar farashin ruwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma wargajewar kasuwannin duniya sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Farashin bitcoin ya fara ne a ranar Litinin, 11 ga Maris da jarin dalar Amurka biliyan 803 kafin rufewarsa a ranar da dalar Amurka biliyan 754.5 yayin da aka tafka asarar dala biliyan 48.4 cikin sa’o’i.

A lokacin rubuta wannan rahoton, farashin ya koma dala dubu 40.3 idan aka kwatanta da farashin dala dubu 39.34 da aka gani a ranar Litinin, 11 ga Afrilu 2022, bisa bayanan shafin diddigin kudaden intanet, Coindesk.

Coinglass kuma ya ba da rahoton cewa sama da dala miliyan 439 aka rasa a zagayen kasuwar crypto a cikin awanni 24.

Hakan ya hada da harkalloli 141,000, wanda daya daga cikinsu ya yi asarar dala miliyan 10 a cinikinsa.

#Jarida Radio

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here