Home Sashen Hausa Ya Kamata 'Yancin Fadar Albarkacin Baki Ya Zama Yanada Iyaka — Firaministan...

Ya Kamata ‘Yancin Fadar Albarkacin Baki Ya Zama Yanada Iyaka — Firaministan Canada Trudeau, Ga Shugaban Kasar Faransa

Ya Kamata ‘Yancin Fadar Albarkacin Baki Ya Zama Yanada Iyaka — Firaministan Canada Trudeau, Ga Shugaban Kasar Faransa

Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce ya kamata ‘yancin faɗar albarkacin baki ya zama “mai iyaka” sannan kuma kar ya “ci mutuncin” wata al’umma.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce Trudeau na bayyana hakan ranar Juma’a, sai dai ya ƙara da cewa za su ci gaba da kare ‘yancin mutane na bayyana ra’ayinsu.

A ‘yan kwanakin nan ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kare zanen ɓatancin da jaridar Chrlie Hebdo ta yi na Annabi Muhammadu S.A.W. da cewa ‘yancin faɗar albarkacin baki ne, abin da ya haddasa jawo ɓacin rai da kisan kusan mutum biyar.

Ƙasashe da ɗaiɗaikun Musulmai a faɗin duniya sun yi Allah-wadai da kalaman na Macron, wanda ya ce “addinin Musulunci na cikin rikici a ko’ina a duniya”.

Sai dai cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Aljazeera, Macron ya ce ya fahimci cewa zanen barkwancin ya ɓata wa wasu rai amma a matsayinsa na shugaba “dole ne ya kare ‘yancin faɗar ra’ayi da na rubutu da na zan-zane”.

“A kodayaushe za mu kare ‘yancin faɗar ra’ayi amma ba maras iyaka ba,” in ji Justin Trudeau lokacin da aka tambaye shi game da ‘yancin nuna zanen ɓatancin Annabi da mujallar Charlie Hebdo ta yi.

“Dole ne mu riƙa girmama sauran mutane kuma kar mu yi ƙoƙarin ɓata ran waɗanda muke zaune tare da su a mahalli ɗaya ko duniya ɗaya.

“Misali, ba mu da ‘yancin da za mu yi ihu a gidan kallo cike da jama’a cewa gobara-gobara, a kodayaushe akwai iyaka.”

Yayin da yake nisanta kansa daga matsayin da Emmanuel Macron ke kai, Trudeau ya buƙaci a riƙa yin taka-tsantsan wurin bayyana ra’ayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: