Home Sashen Hausa YA KAMATA 'YAN NAJERIYA SU BI DOKAR SANYA TAKUN-KUMIN KARIYA DON KAUCE...

YA KAMATA ‘YAN NAJERIYA SU BI DOKAR SANYA TAKUN-KUMIN KARIYA DON KAUCE WA DOKAR KULLE, INJI FADAR SHUGABAN KASA.

YA KAMATA ‘YAN NAJERIYA SU BI DOKAR SANYA TAKUN-KUMIN KARIYA DON KAUCE WA DOKAR KULLE, INJI FADAR SHUGABAN KASA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Fadar Shugaban kasa ta damu da rahoton rashin kiyaye dokar da aka rattaba hanu akai kwanan nan, daya wajabta sanya Takun-kumi da bada tazara a tsakanin al’umma, Fadar tayi roko ga ‘yan Najeriya kan su bada hadin kai sosai don samun Nasaran Manufar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari shiya gabatar da Dokar da kyakkyawar Manufa ba don haka siddan don Musguna wa ‘yan kasa ba.

Fadar Shugaban kasa ta roki Gwamnatocin Jihohi, Sarakunan Gargajiya da Shugaban nin Addini da suma su taka rawa gurin wayar da kai ga Al’umma da Tilasta bin Dokar.

Domin Samun Nasarar haka, Membobin Kwamitin Cutar Korona ya kamata su Lallashi Al’umma don su bada hadin kai ga Gwamnati don ganin ansamu Nasarar kiyaye dokar da kauce wa dokoki masu Tsauri da zasu iya janyo Fushi da rashin Juriya, Game da janyo koma baya kan Manufar sabuwar Dokar.

Gwamnatin Buhari bata son ta sake sanya dokar Kulle a kasar sai dai yazamo dole koda kuwa rai baya so, a Cigaba da karfafa daukan Matakai da bin hanyoyin daza a kauce dokar kullen shine bin Matakai da Kwamitin Shugaban kasa kan cutar Korona ta shimfida.

‘Yan Najeriya sunji ba dadi sosai kafin suka fita daga Dokar Kulle mai Tsoratar wa kuma ita Gwamnati batason jin maganar sake dawowar dokar saboda dayawan ‘Yan kasar bazasu samu abinci dazasu ci batare da sunyi fita sun gudanar da harkokin kasuwanci na yau da kullum ba.

Ana bukatar ‘Yan Najeriya suke sanya Takun-kumin kariya, Wanda Hannaye a kai akai da Sabulu da ruwa tsaftatacce, dama Bada tazara a bainar Jama’a ba a gida kawai ba, da fatan wannan zai taimaka gurin hana yaduwar Cutar Korona.

Duk da ma de Riga kafin cutar na daf da shiga hanu, Kauce wa bin dokokin da Al’umma keyi na durkusa yaki da kwayar cutar.

Dole ‘Yan Najeriya sai sun watsar da kokonton karyata gaskiyar Annobar Cutar ta hanyar bin Dokar sanya Takun-kumi

Muna da aiki na bada kariya ga kan mu, da sauran Al’umma a wannan Mawuyacin hali da Duniya ke ciki na rikicin kiwon Lafiya; Babu wanda yake da rigar kariya na wannan Annobar. Kin bin Gargadin kiwon lafiya da kin bin bada hadin kai ga Dokokin kariya yana mumunar Cutaswa fiye da Alfanu.

Annobar Cutar Korona babbar barazana ce ga Lafiyan Al’umma, Sanya Takun-kumi, bada Tazara a guraren Al’umma da tsaftace wa sun zamo Matakai na dole daya kamata ayi imfani dasu don kiyayen lafiyar Al’umman Kasar mu.

Dole ‘Yan Najeriya suji a ran su cewa Annobar Cutar Korona ba kawai barazana ce ga Lafiya A’umma ba, illa ce kuma ga Tattalin Arzikin kasa da dukkan harkokin Rayuwar yau da Kullum.

Kare Lafiyan Al’umma yana daya daga cikin manyan Hakkin ga duk Gwamnati da tasan abinda takeyi, Gwamnatin nan bazatayi taka wannan Alhakin dake a wuyan ta ba.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
31 ga watan Janeru, 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA.

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA. Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren...

Bazamu sake yin yarje-jeniya da ‘yan bindiga ba saboda sunci amanar mu- Aminu Bello Masari

Ba Za Mu Kara Yin Sassanci Da ‘Yan Bindiga Ba A Katsina, Saboda Sun Ci Amanar Yarjejeniyar Sulhun Har Sau Biyu, Cewar Gwamna Masari Gwamnan...
%d bloggers like this: