Yaƙi da Ta’adanci: Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina ta sake yin Nasara akan Barayin Daji..

Rundunar tayi Nasarar fatattakar Barayin Daji a Batsari tareda kwato Tumaki Ashirin da Tara da Awaki Ashirin da Hudu, Babura Bakwai da Gidan Saka Alburushi mai Daukar Alburushi Guda Talatin mai girman 7.62mm

Da Safiyar Yau din nan DPOn ƙaramar hukumar Batsari ya jagoranci rundunar kan kace kwabo ta “Puff Adder” da “Sharan-Daji” zuwa ƙauyen Shekewa hanyar Shiga dajin Dumburum Inda suka kayi Nasarar fatattakar Barayin Daji da suka gudu da raunikan harbin Bindiga.

Rundunar ta yi kira ga Al-umma da akoda yaushe ta basu bayanan sirri hakan zai taimaka masu wajen gudanar da Ayyukan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here