WAYE THOMAS SANKARA?

_Haruna U. Jahun

A shekarar 2006 lokacin da ake juyayin shekaru sha tara da kisan da aka yiwa tsohon shugaban ƙasar Burkina Faso, Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi ƙarin haske akan irin tuhume-tuhumen da ake yiwa shugaban ƙasar Burkina Faso na lokacin wato Blaise Campaore bisa ga laifukan da ake zarginsa na kitsa kisan gillar da ya yiwa marigayi Thomas Sankara. Haka ma iyalan na Thomas Sankara sun buƙaci a nuna musu inda aka binne maigidan nasu. Rahoton ya ƙara da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci da a gurfanar da waɗanda su ka yi wa Thomas Sankara kisan gilla a kotu sannan a biya iyalansa diyya.

A ƙoƙarinsa na amsa wannan buƙata ta Majalisar Ɗinkin Duniya Blaise Campaore wanda ya jagoranci juyin mulkin ya yi tayin zai baiwa iyalan Sankara kuɗin Faransa har 43,445,000. Sannan zai gina ɗakin tarihi domin tunawa da shi, zai kuma raɗawa titi sunansa domin ake tunawa da shi. Amma iyalan na Thomas Sankara suka ce ba wannan ne ya dame su ba, abin da suke so shi ne sanin ainihin haƙiƙanin abin da ya faru na kashe musu maigida.

Haka aka yi ta fama har zuwa wannan shekara ta 2021 shekaru talatin da huɗu da aiwatar da wannan juyin mulki. A halin da ake ciki kotun soji a birnin Ouagadougou ta Burkina ta fara shari’ar mutane sha huɗu da ake zarginsu da kashe Thomas Sankara. Waɗanda suka haɗa da Blaise Campaore da wasu muƙarrabansa sha uku. Laifukan da ake tuhumarsu da su sun haɗa da yin zagon ƙasa da tsaron ƙasa da kisan kai sannan da ɓoye gawarwakin waɗanda aka kashe. Wanda shi Blaise Campaore yan da wani na hannun damansa Janar Gilbert Diendere suka aiwatar.

Wannan shari’a mai ban mamaki shi ya haifar da wasu mutanen suke tambayar shin waye wannan Thomas Sankara? Wanne irin tasiri yake da shi haka da shekaru talatin da huɗu da kashe shi amma za a fara shari’ar kisan da aka yi masa? Menene dalilin kashe shi, kuma ya aka yi aka kashe shi? Da sauran tambayoyi masu yawa. Saboda haka Tsokaci na wannan mako zai duba wasu daga cikin waɗannan tambayoyi.

Shi dai Thomas Sankara an haifeshi ranar 21 ga watan Disamba, 1949 a garin Yako a lokacin ana kiran ƙasar da suna Upper Volta. Mahaifansa sun so ya zama malamin Cocin Katolika, yana da shekaru sha tara ya shiga aikin soja bayan ɗan horon aikin soja daya samu a babbar sakandiren da ya yi a shekarar 1966. Shekara ɗaya da shigarsa aikin soja sai aka tura shi ƙasar Madagascar domin ba shi wani horon aikin soja. A zaman nasa a Madagascar ne ya ga tashe – tashen hankula daya faru a shekarar 1971 da 1972. A shekarar ta 1972 ya dawo ƙasar ta Upper Volta. A 1974 ƙasar Upper Volta da Mali suka sa zare saboda haka yana cikin sojojin da suka yi yaƙi akan iyakar ƙasarta su da Mali.

A cikin wani littafi da wani mai suna ” A WARRIOR’S TALE” wanda wani marubuci mai suna Kangsen Feka Wakai ya rubuta ya bayyana Thomas Sankara a matsayin “mutumin da ya damu da makomar ƙasarsa matuƙa da kuma ƴanto ta daga hannun ƴan jari hujja da kuma ƴan kama karya bayan baiwa ƙasar ƴanci”. A shekarar 1976 ya zama kwamandan wata rundunar soji mai bada horo a cikin shekarar ne kuma ya haɗu da Blaise Campaore a ƙasar Morocco. Thomas Sankara ya shiga cikin wata ƙungiya ta asiri mai aƙidar tsarin kwaminisanci. Cikin waɗanda suka shiga wannan ƙungiya akwai shi Blaise Campaore da Henri Zongo da Jean-Baptiste Boukari Lingani. A lokacin Kanar Saye Zerbo ne shugaban ƙasar ta Upper Volta.

Himma da kuma ƙoƙarin Thomas Sankara shi ya bashi farin jini da suna sosai a cikin babban birnin ƙasar Upper Volta wato Ouagadougou. Mutum ne mai sha’awar kiɗan jita kuma har ma ƙungiya ce da shi ta masu wasan jita. Sannan yana da sha’awar tuƙa babur. A Satumbar 1981 an naɗa Sankara muƙamin Sakataren yaɗa labarai na ƙasar. Abubuwan da ya yi a wannan muƙami shi ne ya ƙara fito da shi sosai a idon ƴan ƙasar tare da ba shi farin jini musamman tsantsani da rashin ji da kai. Wani abu muhimmi da ya kamata a kawo anan dangane da ƙanƙan da kansa shi ne lokacin da ake taron majalisar ƙasa a ya je zauren taron a kan keke maimakon mota mai tsada tare da rakiyar jami’an tsaro. Ya bar aikin majalisar a Afirilun 1982 saboda wata doka da aka kafa wadda dokar za ta tauye haƙƙin ma’aikata.

A Nuwambar 1982 aka yiwa shugaba Kanar Saye juyin mulki wanda Manjo Dokta Jean-Baptiste Ouedraogo ya jagoranta bayan nasarar juyin mulkin sai ya naɗa Thomas Sankara a matsayin Firayim Minista a Janairun 1983 amma tafiyar ba ta je ko’ina ba, saboda wata biyar kacal da naɗa shi sai aka kore su shi da abokansa Henri Zongo da kuma Jean-Baptiste Boukari daga muƙamansu sanadiyyar saɓanin fahimta da suka samu akan gudanar da gwamnatin. Sannan ba kawai an kore su bane har an yi musu ɗaurin talala, an tsare kowa a gidansa. Wannan ɗaurin talala da korar da aka yi musu ya jawo tarzoma a ƙasar sanadiyyar haka aka sake wani juyin mulki kuma aka miƙa ragamar mulkin ƙasar ga Thomas Sankara. Ya zama shugaban ƙasa yana shekara 33 yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙasa masu ƙarancin shekaru a lokacin. A wannan lokacin guguwar juyin mulki tana tsaka da kaɗawa a nahiyar Afirka. Me ya bambanta Thomas Sankara da sauran?

Sankara yana ganin cewa shugabancin da aka ɗora masa hanyace ta tabbatar da tsare-tsarensa na tabbatar da juyin juya hali a tsarin dimokaraɗiyyar Afirika. Dangane da haka ya zama mai matuƙar kishin Afirka da kuma kyamatar turawan mulkin mallaka, mahandama masu ci da gumin ƙasashen Afirka. Kafin ya hau mulkin, ƙasarsa ta Upper Volta tana ɗaya daga cikin ƙasashen da a duniya aka barsu a baya ta kowacce fuska jahilci ya yi katutu a ƙasar da kashi 90, a harkar lafiya babu komai, ita ce ƙasar da tafi yawan mace-macen ƙananan yara, likita ɗaya yana duba marasa lafiya dubu hamsin!. Yana hawa kan kujerar mulki abin da ya fara shi ne ƙaddamar da juyin juya halin ta hanyar yaƙi da cin hanci da rashawa. Wanda shi ne babbar matsalar ƙasaahen Afirka, haka kuma ya bada himma wajen kyautata dazuka da kuma fito da hanyoyin da za a yaƙi yunwa. Ya kuma mai da hankali wajen inganta ilimi da haɓaka shi. Hakanan sha’anin lafiya ya samu kulawa ta musamman waɗannan sune abubuwan da yafi baiwa fifiko. Banda gina sabbin tituna da sauran abubuwan inganta rayuwa.

A bikin cikarsa shekara ɗaya da juyin juya halin ne ya canza sunan ƙasar daga Upper Volta zuwa Burkina Faso wanda a harshen ƙasar yana nufin ƙasar masu gaskiya. Shugabancin Sankara ne ya sa ƴan Burkina Faso suka san kansu, mutuncinsu da kuma martabar ƙasarsu. Shi ne wanda ya sa musu aƙidar cewa “babu wani abu da zai gagari mutum matuƙar ya duƙufa akan zai yi”. Rayuwarsa ta zama mai sauƙi da babu almubazzaranci sannan shi ne shugaban da ya bayyana kadarorinsa da ya mallaka wanda a lokacin albashin sa dala ɗari huɗu da hamsin, sai mota da keke da jita guda uku a firij. Ana cewa shi ne mafi talauci a shugabannin duniya na lokacin. Duk tsare-tsarensa da manufofinsa na yadda ƴan ƙasa da kuma talaka zai ji sauƙin rayuwa ne.

A Fabarairun 1984 ya soke biyan haraji da kuma noman dole da talakawa suke yiwa masu sarauta sannan a Agustan shekarar ya ayyana cewa ƙasa da albarkatunta ta zama mallakar gwamnati. A Oktoban shekarar aka haramta biyan jangali a Nuwambar shekarar kwanaki sha huɗu tsakani aka yiwa yara sama da miliyan biyu da ɗigo biyar allurar riga kafin sanƙarau da shawara da kuma kyanda. Sannan Sankara ya ƙaddamar da shirin dasa bishiya miliyan goma domin rage kwararar hamada, zuwa ƙarshen 1986 shirin yaƙi da ciwon dundumi ya kankama. Ya gina ɗakin karɓar magani a ƙauyuka 5,384 cikin ƙauyuka 7,500 da suke. Hakanan kuma an sa yara a makarantar wanda har alƙaluman yara masu zuwa makaranta ya ƙari daga kashi 6 zuwa kashi 22.

A kuma siyasar sa da ƙasashen waje, Thomas Sankara shi ne shugaban da bai yarda da karɓar taimako daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ba kamar Bankin ba da lamuni na duniya. Ko da yake yakan karɓi taimako daga wasu hanyoyin amma yana taka-tsantsan da kuma ƙoƙarin ƙasar sa ba ta dogara da irin wannan taimako ba kacokaf ta hanyar bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga da fito da dabarun neman taimako.

Mai yiwuwa yadda ya hana ƴan barandar mulkin mallaka na cikin ƙasar watayawa tare da shigewa turawa yamma hanci yasa ranar 15 ga Oktoba 1987 aka yi masa juyin mulki. Ana zargin da hannun ƙasar Faransa wato ƙasar da tayi wa Burkina Fason mulkin mallaka aka ƙulla yi masa juyin mulkin. Kuma abin mamaki abokin gwagwarmayarsa Blaise Campaore da shi aka haɗa yi masa juyin mulkin. Sankara an kashe shi tare da wasu muƙarraban gwamnatinsa su sha biyu.

Wani abu da yafi damun iyalansa da masoyansa shi ne yadda aka kashe Thomas Sankara aka kuma binnesu da har yau babu mahalukin da zai ce ga ƙabarinsu. Wannan ne yasa bayan tayin ba da kuɗin da Blaise Campaore ya yi musu shekaru sha biyar da suka wuce su ka ce ba sa buƙata. Abin da suke so a bayyana musu yadda al’amarin ya kasance sannan kuma a nuna musu kabarinsa.

Shugabancin Sankara bai taƙaita ga ƙasar Burkina Faso ba, shugabanci ne da ya baiwa sauran ƙasashen Afirka ƙarfin guiwa ta yadda za su tashi su tsayu da ƙafafunsu. Shekaru talatin da huɗu da kisan gillar da aka yi wa su Thomas Sankara sai yanzu aka fara shari’ar bayan Blaise Campaore ya yi mulkinsa na shekaru ashirin da bakwai domin ya sauƙa ne a shekarar 2014 bayan boren da ƴan ƙasar su ka yi masa. Komai zai faru a wannan shari’a? Lokaci ne kawai zai tabbatar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here