Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

“Shuaban yan uwa musulmi mabiya mazhabin shi’a, “sheikh Ibrahim Al-zakzaky; ya bada umarnin bude rumbun abinci kusan tirela guda, domin rabawa al’umma marasa karfi kyauta a shirye-shiryen shiga watan ramadana.”

Biyo bayan tabbatar da wannan gagarumin tallafawa marasa karfi da shehin yayi, majiyar ya shaida cewa, ba wannan bane karo na farko da shehin ya keyi.”

“A cigaba da farauto bayanai, ganau ya tabbatar da cewa, shehin ya kwshe shekaru yana wannan rabon abincin, har lokacin da gwamanatin Najeriya ke tsare da shi shehin ya bada umarnin a cigaba da wannan rabon abincin kamar yadda aka saba yi.”

“Wannan al’amarin sanan nan Abu ne, musamman ga al’ummar da suke makwaftaka da shi shehin malamin a lokacin da yake zaune a unguwar gyallesu cikin birnin zariya.”

A shekarar du biyu da sha biyar kimanin shekaru bakwai kenan rundunar sojojin Najeriya ta afkawa malamin a gidansa inda suk kashe daruruwan mabiyansa suka harbeshi da matar sa sana suka kamashi inda ya kwashe fiye da shekaru biyar a tsare, bisa tuhumar sa da laifin tsare hanya, wanda daga bisani kotun daukaka kara ta wanke shi gami da sallamarsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here