AL’AJABI: Wata Mata Ta Kona Al’aurar Mijinta

Wata matar aure da ta kona wa mijinta al’aura a Jihar Kano ta gurfana a gaban  Kotun Majistare da ke zamanta a Gyadi-Gyadi.

Ana tuhumar matar, ’yar garin Abu Dakaya na Karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano da yin sanadiyyar kona gaban mijin nata ne da tafasasshen ruwa.

Magidancin ya shaida wa kotu cewa yana neman a bi masa hakkinsa kasancewar a yanzu gabansa ma ya samu matsala.

Mai gabatar da kara kuma Lauyar Gwamnati, Asma’u Ado ta shaida wa kotu cewa matar ta zuba wa mijinta tafasasshen ruwa a buta da gangan inda shi kuma cikin rashin sani ya yi tsarki da ruwan hakan ya janyo ya samu rauni a gabansa.

Shi ma mai kara, Gaddafi Sani ya bayyana cewa a lokacin da lamarin ya faru ya umarci matar tasa ta dama masa kunu.

“A gabana ta dora ruwan zafi sai dai lokacin da na zo na tambaye ta kunun sai ta yi min shiru.

“Ni kuma sai na ga buta a gabanta sai na dauka don zagawa bayan daki.

“Ni ban sani ba ashe wannan ruwan zafin kunun da ta dora a wuta shi ta juye a butar ni kuma sai na je na yi tsarki da shi. A nan na babbake gabana.

“Lokacin da na tambaye ta sai ta kyalkyace da dariya sannan ta ce wai ta yi hakan ne don ba ta son haihuwa da ni.”

Ya ce yana neman kotu ta bi masa hakkinsa kasancewar a yanzu gabansa ma ya samu matsala.

Sai dai wacce ake zargin tamusanta laifin da ake zargin na janyo mummunan rauni ga mijinta, laifin da ya saba wa sashe na 245 a cikin Kundin Shari’ar final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Datti Sa’ad ya bayar da aumarnin tsare wacce ake zargi a gidan yari tare da dage sauraren shari’ar zuwa ranar 2 ga watan gobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here