Advert
Home Sashen Hausa Wata Kotu a Kano ta dakatar da 'yansanda kamo Danjarida Nasiru Salisu...

Wata Kotu a Kano ta dakatar da ‘yansanda kamo Danjarida Nasiru Salisu Zango.

Daga: Fahad Kabir Maitata

Wata babbar kotu a jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a, Abdu Maiwada Abubakar, ta bayar da umarnin dakatar da kama Dan Jarida Nasir Salisu Zango na wucin gadi ga kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Sama’ila Sha’aibu Dikko da dan sanda mai mukamin Inspector mai suna Friday cewa kada su kuskura su kama dan jaridar.

Dan jaridar cikin shirinsa da yake gabatarwa a gidan Rediyon Freedom ya fallasa yadda wasu daga cikin jami’an ‘yan sanda ke karbar makudan kudade daga hannun wasu ‘yan kasuwa daban-daban a jihar wanda ake kamasu kuma a karbi kudin beli daga hannun su ko ‘yan uwansu.

Bayan fitar da rahotan an yi zargin cewa, rundunar ‘yan sanda tayi kokarin kamo Dan jarida Nasir Salisu Zango.

Daga bisani kuma Zango ya shigar da kara, kuma ya dauki lauya domin kare shi, bayan sauraran lauyansa mai suna Barista Abba Hikima, Alkalin ya bada umarnin hana kama shi a yau Alhamis. Sai dai an dage cigaba da sauraren karar zuwa 19 ga watan Nuwamba.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...