Wata kotu a Iraƙi ta ba da umarnin kama Trump game da kashe Soleimani

Wata kotu a Bagadaza ta ba da umarnin kama shugaban Amurka Donald Trump a wani ɓangare na binciken da suke yi kan kisan babban kwamandan Iraƙi.
Abu Mahdi al-Muhandis, wanda mataimakin shugaban masu goyon bayan Hashen al-Shaabi ne, ya mutu a cikin harin da ya yi sanadiyyar mutuwar janar din Iran Qasem Soleimani a filin jirgin saman Bagadaza a ranar 3 ga watan Janairun 2020.
Trump ne ya ba da umarnin harin da aka kai kan motocinsu, wanda daga baya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.
Masu tattaro bayani na Majalisar Dinkin Duniya kan kisan azarbabi sun ce wannan kisan da aka yi wa mutanen ya saba ka’ida.
Kafin nan Iran ta ba da umarnin kama Trump tin a watan Yuni, tare da bai wa ‘yan sandan ƙasa da ƙasa umarmim kama shi da kuma duka ‘yan sandan duniya umarnin kamashi