Wata Gobarar a katsina ta laƙume dukiya mai yawa;

Sati biyu bayan faruwar gobara a Babbar kasuwar Katsina, yau Litanin kuma wata gobarar ta tashi a Unguwar sabon titin kwaɗo dake cikin garin na katsina inda ta laƙume Shaguna da dukiya mai dunbun yawa aciki.

Gobarar da ake zaton ta faru ne sanadiyyar wani mei saida abinci da yake amfani da tukunyar Gas domin dafa abinci, inda tukunyar ta kwace takuma shafi shagunan dake kusa dashi.

Anshawo kan matsalar inda jami’an kashe gobara suka bada himma domin ganin wutar bata ƙetara unguwanni ba, yazuwa yanzu dai ba a Tantance yawan asarar da akayi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here