Wata babbar kotu dake a Abuja tabada Umarnin garƙame Abdulrashid Maina gidan gyara halinka

Wata babbar kotu dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta bada umurnin a tasa keyar Abdulrashid Maina zuwa gidan gyaran hali dake Kuje Abuja.

Zaharaddeen Mziag@katsinacitynews

Shari’ar Maina wacce aka dawo da saurarar ta a ranar Juma’ar nan 4 ga watan Disamba 2020, lauyan dake wakiltar Maina mai suna Adaji Abel, shi ne ya fara janyewa inda Maina ya sanya wani sabon lauya wanda kuma ya roki kotu a daga shari’ar domin ya sami damar karanta hujjojin sa akan tuhumar da ake yiwa Maina.

Abulrasheed Maina, wanda hukumar EFCC ta yanke masa hukunci akan satar kudi da adadin su yakai naira Biliyan biyu (N2B), ya tsere ne bayan da aka bada Belin sa inda ya tsallake ya gudu Jamhoriyar Nijar.

An kuma dawo da shi gida Najeriya a jiya Alhamis 3 ga watan Disambar 2020 bayan sati biyu da kotu ta soke bada Belin sa tare da bada umurnin a kamo shi kuma shari’ar sa za ta cigaba ko ba ya nan har zuwa lokacin da jami’an tsaro za su kamo shi.

A yau Juma’a 4 ga watan Disamba 2020 da misalin karfe 8.27 na safiya aka kawo Maina gaban kotu domin a fara shari’ar da karfe 9 na safe yanzu haka kuma Alkali Jostis Okon ya bada umurnin a tura Maina zuwa gidan gyaran hali dake Kuje Abuja har zuwa ranar da za’a zo a cigaba sa shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here