WASU MAHARA SUN KASHE MUTUM BIYU A YANKIN BATSARI.

A daren jiya talata 20-07-2021 da misalin 7:50pm wasu ‘yan bindiga su ukku suka tare hanyar Batsari zuwa Watangadiya, inda suka harbe wasu matasa dake kan bubur ɗaya da sukayi goyon ukku.
A tattaunawar mu da wani da ya sha da kyar Malam Habibu Dan Kirtawa yace; “Suna cikin tafiya kan babur bayan sun sha kwanar da ta nufi garin su, wato kauyen Watangadiya, sun isa dai-dai wata giginya, kawai sai sukaji harbi daga bayansu, inda aka harbi mai tukin babur din mai suna Sabitu Burosa kai, nan take ya cika, su Kuma suka ruga a guje a kafa, inda Kuma aka bisu da harbi nan ma aka sake harbe Isiya Jafaru, dukkansu ‘yan cikin Watangadiya ne. Daga bisani Kuma suka dauke babur din tare da wasu Kaya suka gudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here