Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a daren Asabar sun kashe kimanin mutane 14 a garin Kaya, wani kauye da ke karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yamma. lokacin da ‘yan fashin, wadanda aka ce suna shirin daukar fansa ne, suka afka wa karamin kauyen suka kashe mutanen kuma suka bankawa motoci wuta.
Wani mazaunin yankin, wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Suleiman, ya ce mutane tara sun samu raunuka.
A cewarsa, a safiyar ranar Juma’a, wasu ‘yan banga a yankin sun kashe wasu’ yan ta’adda da suka kai hari a wani kauye da ke makwabtaka da su.
”‘ Yan fashin sun far wa kauyen mu ne don daukar fansar kisan da mambobin mu da ‘yan banga mu ka yi bayan sun sace tare da kashe mutum daya a ranar 1 da 2 ga watan Janairu. Don haka suka dawo cikin dare ranar Asabar a kan babura suka kashe mutane 14, ”inji shi, kamar yadda Premium Times ta rawaito.