Advert
Home Sashen Hausa WASU MAHARA SUN KAI FARMAKI BATSARI TA JIHAR KATSINA.

WASU MAHARA SUN KAI FARMAKI BATSARI TA JIHAR KATSINA.

Daga misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news

Da misalin karfe tara na daren ranar talata 17-08-2021 wasu gungun ‘yan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka yima unguwannin Tanki da unguwar Malamai dake cikin garin Batsari a jihar Katsina dirar mikiya.

Sunyi harbe-harbe tamkar a fagen fama wanda ya ruda mafi yawan al’umar ciki da wajen garin Batsari, sun kama mutane masu yawan gaske, mata da yara kanana da magidanta.

Sai dai cikin taimakon Allah, da yawan mazan da suka dauka sun kubuto. Amma yanzu akwai mutane goma hannun su, matan aure bakwai, yaran goye biyu da magidanci guda daya. Sai dai mutane ukku sun gamu da ajaliyyar su sakamakon harin.

Dattijiya daya wacce aka labarta mana tana da hawan jini, kuma sakamakon harbe-harben jikinta ya motsa wanda nan take rai yayi halin shi, sai mutane biyu maza magidanta mazauna unguwar kwana ukku wadanda ake zargin sun yi taho mu gama ne da harbe harben da aka rikayi.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa lokacin da jami’an tsaro suka tunkaro su a guje sai wani ya harba bindigar toka, dalili kenan da yasa jami’an tsaro suka yi harbin da yayi sanadiyyar rasa rayukan mutanen biyu.

A wani labarin kuma, dandazon ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Dankar dake cikin yankin na Batsari, duka a ranar ta talata, inda suka sace dabbobin da suka hada da shanu, tumaki da awaki da yawansu bai gaza ma dari ukku ba, sunyi harbe-harbe kuma sun balle shaguna sun wasashe kayyakin masaruhi sun dora kan babura sun tafi salin alin
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: