Wasu jaridun Najeriya na shirin fitar da rahotannin ɓata wa Buhari suna’

Shugaba Buhari

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan yaɗa labarai, Femi Adesina ya ce ya zama lallai ya fargar da ƴan Najeriya kan wata manaƙisa da wasu kafofin yaɗa labarai na intanet ke shiryawa don ɓata wa Shugaba Buhari suna.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Adesina ya ce a kwanan nan ne shafukan za su fara fitar da labarai da rahotanni da suka shirya musamman don rura wutar rikici a ƙasar.

Ya ce suna da niyyar nuna Shugaban a matsayin mai nuna son kai da nuna ɓangaranci. Wannan ya saɓa wa alƙawarin da ya yi wa ƴan Najeriya na zama na kowa.

Adesina ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa masu son tada zaune tsayen sun saye shafukan intanet da jaridun da ke shirin fitar da rahotannin da ke zargin shuga Buhari da nuna wariya ga wani addini ko ɓangare.

Mista Adesina ya ce rahotannin sun ƙunshi labaran ƙarya da ke nuna cewa Buhari ya daɗe yana amfani da ƙarfin ikonsa wajen kare wani ɓangare daga laifukan kisa da garkuwa da mutane da fashin daji a kudancin ƙasar da yankin tsakiya da wasu jihohin arewacin Najeriya, a cewar Femi.

Haka kuma, ya ce rahotonnin na zargin Buhari da bai wa wasu zaɓaɓɓun mutane muƙamai masu daraja a ƙasar.

Femi ya yi kira ga ƴan Najeriya da su farga su gane cewa duka waɗannan zarge-zarge ƙarya ne.

Ya ce mutanen ba su da wata manufa illa ta neman mulki da son tara dukiya ba a bisa ƙa’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here