Wassanni: Gwaji ya sake tabbatar da Salah yana ɗauke da
korona
Daga: Abdulhakim Muktar
Sakamakon gwajin da aka sake yi wa ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya nuna yana ɗauke da korona yayin da ya tafi bugawa ƙasarsa Masar wasa.
Ɗan wasan mai shekara 28, a makon da ya gabata ne gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da korona.
A ranar Laraba, hukumar kwallon Masar ta tabbatar da ɗan wasan ya kamu da korona.
A ranar Lahadi ne kuma Liverpool za ta karɓi bakuncin Leicester City kafin ta haɗu da Atalanta a gasar zakarun Turai a ranar 25 ga Nuwamba.