Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase, ya zargi wasu jami’an ‘yan sanda da hannu wajen haɗa baki da ‘yan bindiga ana kai hare-hare a Arewacin Najeriya.

Wase wanda ɗan jam’iyyar APC ne daga jihar Filato, ya yi wannan zazzafan zargin a ranar Talata, inda a zauren majalisa ya gabatar da roƙon gaggawa dangane da hare-haren da ‘yan bindiga su ka kai garin Pinau da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wase, a jihar Filato.

Wase ya kawo misalan wurare uku inda ƴan sanda su ka saki ƴan bindiga, masu garkuwa da kuma ƴan fashi da makami.

Ya yi zargin cewa wasu jami’an tsaro na haɗa baki da mahara, don kawai a riƙa yin maƙarkashiya ga ƙoƙarin da wannan gwamnati ke yi wajen daƙile matsalar tsaro.

“Jami’an tsaro ba su taimakawa domin a ga an kawar da wannan matsalar.

“Lokacin da ‘yan bindiga su ka saci matar hakimin garin mu, ‘yan sa-kai sun bi su har cikin Jihar Taraba, su ka ceto matar, kuma su ka kamo ‘yan bindigar. To abin takaici, a yanzu haka ‘yan sanda sun sake su bayan ‘yan sa-kai sun damƙa masu su.

“Na biyu, kwanan nan an kamo wani da aka gano ya na haɗa kai da ‘yan bindiga a yankin mu. Ya yi magana inda ya amsa zargin da ake masa, kuma an yi rikodin ɗin bidiyon sa ya na maganar. To yanzu haka shi ma wannan ‘yan sanda sun sake shi.”

Na uku kuma Wase ya bada misalin wani ɗan uwan sa da aka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna. An kama ɗan garkuwar da ya riƙe shi, amma shi ma ‘yan sanda sun sake shi.

Ya ce ya shaida wa Gwamna Nasir El-Rufai, amma ya sanar da shi cewa ‘yan sanda sun lalata lamarin, saboda hatta mai binciken laifin ma an canja shi.

Da ya ke sa bakin sa, Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Toby Okechukwu ya bayyana cewa Najeriya ba ta taɓa afkawa cikin irin wannan bala’in a baya ba.

Shi kuma Ɗan Majalisa Nasir Ali daga Kano, mamakin shugabannin tsaro ya yi ganin yadda ba su iya jibge jami’an tsaro su magance matsalar tsaro, amma sai su jibge su a wurin kula da zaɓe.

Ya buga misali da yadda aka jibge sama da jami’an tsaro 30,000 a jihar Anambra a lokacin da wurare irin su manyan titinan Arewa ke buƙatar jami’an tsaro, amma ba a tura ba.

Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu ya ce ya yi farin ciki, ganin yadda wannan matsalar masu garkuwa da mutane ta fara shafar mambobin APC.

“Ni dai ina farin ciki da masu garkuwa su ka taɓa ‘yan uwan mutum na shida a jerin masu mulkin Najeriya. Wannan zai tabbatar mana da cewa gwamnatin APC ta gaza kawai.

Sai dai kuma Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya rufe masa baki da tsawa, inda ya nuna masa cewa bai kamata a maida matsalar tsaro batun siyasa ba.

A ƙarshe Majalisa ta amince za ta binciki matsalar tsaro a ƙasar nan.

Premium Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here