Wasa nawa za a dakatar da Messi bayan jan kati a Spanish Super Cup?

bbc Hausa

Ranar Lahadi aka yi wa Lionel Messi jan kati a wasan karshe da Athletic Bilbao ta lashe Spanish Super Cup kuma na uku jumulla.

Athletic ta yi nasara ne da ci 3-2, bayan karin lokaci da suka tashi 1-1, kuma Athletic ce ta fitar da Real Madrid a wasan daf da karshe da ci 2-1.

Wannan ne karon farko da aka bai wa Messi jan kati a Barcelona a wasa 753 da ya yi a kungiyar a dukkan fafatawa.

Koda yake shi ne karo na uku da dan kwallon ya karbi jan kati a tarihin sana’arsa ta kwallon kafa.

Mai shekara 33 ya fara karbar jan kati a wasan da tawagarsa ta Argentina ta yi da Hungary a 2005.

Ya kuma karbi na biyu a Copa America wasan neman mataki na uku a 2019 a wasa tsakanin Argentina da Chile.

Watakila a dakatar da Messi buga a kalla wasa hudu da zai iya shafar La Liga da sauran kofunan gaba da ake buga wa a Spaniya.

Kawo yanzu Messi shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Spaniya mai 11 a raga, kuma Barcelona tana ta uku a teburin gasar bana ta La Liga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here