Advert
Home Sashen Hausa WARWARA: Mufti Menk ya yi karin haske game da hotonshi da Jaruma...

WARWARA: Mufti Menk ya yi karin haske game da hotonshi da Jaruma dake yawo a shafukan sadarwa.

A cikin makon nan ne dai aka dinga ganin hotunan fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan wanda yake bi kasa-kasa domin da’awa da kuma kira ga al’ummar Musulmi, Mufti Menk, da Jaruma mai kayan mata, wacce tayi fice wajen jawo cece-kuce a shafukan sadarwa sakamakon bidiyo, hotuna da maganganu da ta saba yi wadanda ba su dace ba.

A jikin hoton dai an nuno fitaccen Malamin a cikin jirgi tare da Jaruma sun dauki hoto, duk da dai alamun da suka nuna babu fara’a sosai a fuskarshi, amma ita Jaruma an nuno fuskarta cikin fara’a da annushuwa da wannan hoto da ta dauka da Malamin.

Fitar wannan hoto ke da wuya mutane suka yi ta tofa albarkacin bakinsu, inda hakan ya sanya wani ya yiwa Malamin tambaya a wata manhaja ta tambayoyi dangane daa wannan hoto.

Mufti Menk da Jaruma…

Hoton Mufti Menk da Jaruma mai kayan mata da suka dauka a Ethiopian Airlines

Mufti ya nuna bashi da masaniyaa akan wacece ita Jaruma din ma, ya bayyana cewa shi kawai yana zaune ta zo ta nemi ya dauki hoto da ita, ya ce bayan daukar hoton bai jima a wajen ba ma aka zo aka canja masa mazauni, saboda ma’aikatan jigrin suna ganin wajen bai kamace shi ba.

Malamin ya bayyana cewa sun dauki hoton ne a lokacin da ya taso daga birnin Addis Ababa zuwa Abuja, a jirgin Ethiopian Airlines, inda ya kara tabbatar da cewa shi bashi da masaniya dangane da kowacece ita, ga dai yadda hirar su tta kaya, mai tambayar ya bayyana cewa:

Sheikh, akwai wani hoto da kai da Jaruma, yaushe ne aka dauke shi? ~ Mai tambaya

Wacece wannan? ~Mufti Menk

Budurwa ‘yar Najeriya da ka zauna kusa da ita a jirgi. ~ Mai tambaya

Eh na tuna, a lokacin da muka taso daga Addis zuwa Abuja a Ethiopian Airlines kwanannan, akwai wata mata dake zaune a kusa dani. Bani da masaniya ko wacece ita, amma abinda zan iya tunawa ina zama, ta nemi na dauki hoto da ita. Cikin mintuna kalilan wata ‘yar uwa cikin Hijabi ta zo gare ni ta ce, “Sheikh, akwai kujera wacce babu kowa a layin gaba, zai fi dacewa ka zauna a wajen”, aikuwa haka na koma waccan kujerar. ~ Mufti Menk

Jaruma mace ce da tayi suna a Najeriya ~ Mai tambaya

Tsaya kafin ka kai gaba, bari na sake bayani dakyau akan cewa bani da masaniya akan kowacece ita ko kuma sunan da take dashi. Ma’aikatan jirgin ne suka bani wannan kujerar, kuma daga baya suka canja mini da wata. Ina rokon Allah ya ganar da ita da mu duka zuwa hanya madaidaiciya. ~ Mufti Menk

Ameen, nagode da lokacin da ka bayar da kuma bayani Sheikh ~ Mai tambaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: